Hajjin bana: NAHCON ta zo kano domin duba Shirin da hukumar jin dadin alhazai ta yi

Date:

Daga Sayyadi Abubakar Gwagwarwa
Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Dambatta, ya karbi bakuncin tawagar hukumar NAHCON karkashin jagorancin Alhaji Usman Aliyu Shamaki, Daraktan duba aiyuka da bin ka’ida a yau Alhamis a Kano.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da Jama’a ta Hukumar Jin dadin alhazai ta jihar kano Hadiza Abbas Sanusi ta sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.
 Tawagar ta zo Kano ne domin duba dukkan kayayyakin da ake bukata domin gudanar da aikin hajjin bana cikin nasara kuma sun ji dadin yadda shugaban tawagar ya mika godiyarsa ga Sakataren zartarwar hukumar bisa kyakkyawar tarba da aka yi musu.
 A nasa bangaren, sakataren zartarwar Hukumar Abba Muhd Danbatta ya godewa tawagar bisa wannan ziyara tare da yin alkawarin ci gaba da shirye-shiryen da zasu sanya a samu cigaban aikin Hajjin bana.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a farkon makon nan a wani taron manema labarai Sakataren zartarwar hukumar Muhd Abba Danbatta ya bayyana cewa hukumar ta Shirya caf domin tunkarar aikin Hajjin bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...