Mahukuntan kasar Senegal da kungiyoyin farar hula a Najeriya, sun yi alla-wadai da kiran da gwamnatin Ukraine ta yi wa ‘yan kasashen yammacin Afrika da su taimaka ma ta a yakin da take yi da Rasha.
Bayanai sun nuna cewa an samu mutane da dama da suka amsa kiran na jami’an gwamnatin Ukraine a wasu kasashen Afrika, domin yaki da Rasha.
Ma’aikatar harkokin wajen Senegal, ta ce sakon da ofishin jakadancin Ukraine ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bukaci ‘yan kasar su tallafawa kasarsa a yakin da ta ke yi da Rasha.
Ofishin a sakon ya nemi duk wanda ya ke da aniyar taimakawar ya bada sunan shi da lambar waya da adireshin email.
Tuni dai aka samu kuma mutum 36 ‘yan Senegal da suka sanya hannu a kan takardar nuna aniyar taimakon Ukraine din.
BBC Hausa ta Rahotanni sun bayyana cewa an samu wasu ‘yan Najeriya da suka kai kan su ofishin jakadancin Ukraine da ke babban birnin kasar Abuja, tare da jaddada mubaya’a ga kasar domin yakar sojojin Rasha.
Sai dai jami’an ofishin sun shaida musu cewa kowanne zai biya dala 1,000 na sayan tikitin jirgi da bisar balaguron.