Rikicin APC a Kano: Tsagin Shekarau za su ɗaukaka ƙara

Date:

Tsagin Sanata Ibrahim Shekarau a jam’iyyar APC a Jihar Kano da ke rikici da na Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya ce shugabancin ɓangaren gwamna ne halastacce.

Shugaban tsagin, Ahmadu Haruna Zago, wanda ke samun goyon bayan tsohon Gwamna Sanata Ibrahim Shekarau, ya faɗa wa BBC Hausa cewa za su yi biyayya ga hukuncin amma za su ɗaukaka ƙara.

“Za mu ɗaukaka ƙara mana, ai bin umarnin daban kuma ɗaukaka ƙara daban,” in ji shi. “Lauyoyinmu na nazari kan hukuncin kotun.”

Hakan na nufin Kotun Ƙoli ce za ta raba gardama idan suka ɗaukaka ƙarar, kasancewar Kotun Ɗaukaka Ƙara ce ta yi hukuncin na yanzu.

A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce Babbar Kotun Abuja ba ta da hurumin yin hukunci kan rikicin sannan kuma ta ce shugabancin Abdullahi Abbas ne halastacce – ba na Haruna Zago ba.

A makon da ya gabata ne tsagin Shekarau ya yi watsi da wani yunƙurin sulhu da jam’iyyar ta ƙasa ta yi, inda ta naɗa Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamatin sasanta rikicin da suke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...