Gwamnatin Jihar Sokoto ta musanta Yunkurin Kashe Gwamna Tambuwal

Date:

Gwamnatin Jihar Sokoto mai fama da hare-haren ‘yan binidga a arewacin Najeriya ta musanta cewa an jikkata Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da aka ce an kai wa tawagarsa a yankin Sabon Birni.

Wata sanarwa da matamakin gwamnan kan kafafen yaɗa labarai Muhammad Bello ya fitar ta ce duk da cewa gaskiya ne gwamnan da tawagarsa sun kai ziyara Sabon Birni ranar Juma’a amma “lafiya ƙalau”.

Rashin tsaron:Buhari ya tura Shugabanin Hukumomin tsaro jihohin Katsina da Sokoto

Wasu rahotanni da Daily Trust ta tattara sun ce ‘yan fashin daji sun sake kai hari a yankin ne inda suka kashe mutum uku tare da jikkata wasu da dama kwana biyu bayan sun ƙona mutum kusan 30 a cikin motar bas.

Sanarwar ta tabbatar da cewa Gwamna Tambuwal ya je Sabon Birni ne domin jajanta wa mazauna yankin kan harin da aka kai wa fasinjojin kafin sake kai wani harin a ranar Juma’a.

Labarin da ake yaɗawa (na raunata gwamna) ba gaskiya ba ne, wabda wata kafar labarai ta “Critical Times.” ke yaɗawa,” a cewar sanarwar.

Harin wanda shaidu suka faɗa wa BBC Hausa cewa ya faru ne da safiyar Litinin ya harzuƙa ‘yan Najeriya, har ma suka dinga sukar Shugaba Buhari kan tafiya taron ƙaddamar da littafi a Jihar Legas yayin da lamarin ke faruwa.

2 COMMENTS

  1. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. מכוני ליווי

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...

Gwamnatin Kano Ta Karyata Rahoton Cibiyar Wale Soyinka Kan Take ‘Yancin ‘Yan Jarida

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahoton da...

Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Cire Maryam Sanda Daga Jerin Wadanda Za a Yi Wa Afuwa

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin a...

Majalisar Kano ta buƙaci a soke ɗaukar aikin kwastam da aka yi a kwanan nan

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga dukkan...