Daga Nasiba Rabi’u Yusfu
Gwamnonin jam’iyyar APC sun fara tuntubar ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), da nufin ya shawo kan shugaban kasa, Muhammadu Buhari yaƙi amincewa da dokar zaɓe da aka yiwa gyara wadda majalisar dokokin kasar ƙasa ta zartar a ranar Talatar data gabata.
Gwamnonin APC na karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu. Shi ma Malami dan jihar Kebbi ne kuma ana ta rade-radin za’a baiwa Malamin takarar gwamna kebbin a 2023.
Wani hadimi ga daya daga cikin gwamnonin APC ya shaidawa jaridar PUNCH cewa kamar sauran kudirorin da aka mika wa shugaban kasa, ana sa ran Buhari zai mika wa Malami kudirin dokar zabe domin neman shawararsa ta fuskar doka.
Dama dai an dade ana ta cece-kuce akan batun sabuwar dokar wadda ake ganin bazata yiwa gwamnonin daɗi ba ,shi yasa suke ta sukar dokar tare da bin duk wata hanya da za su kawo naƙasu ga dokar.