Rashin cika ƙa’ida: Gwamnatin Kano ta Rufe Wani Kamfani

Date:

Daga Zara Jamil Isa

 

Hukumar kare haƙƙin mai saya da mai sayarwa ta jihar kano ta rufe wani kamfani mai suna C-PIN (CHEMICAL IND) dake unguwar dakata a ƙaramar hukumar Nasarawa bisa ƙin bin ƙa’idojin hukumar .

Shugaban hukumar Gen. Idris Bello Dambazau mai ritaya shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa Kadaura24 a ranar latabar nan.
Gen. Idris Dambazau ya ce kamfani ya gaza cimma ƙa’idojin da suka gindaya musu domin ingata abubun da suke sarrafawa domin amfanin al’ummar jihar kano.
Yace dokar data kafa hukumar ce ta bata ƙarfin ikon rufewa ko daukar matakan da suka dace akan duk wani kamfamin ko dai-daikun yan kasuwa da suke sayarwa ko samar da kayan da zasu iya yin illa ga rayuwar al’ummar jihar kano.
Idan za’a iya tunawa hukumar tana aiki ba dare ba rana domin maganin bata gari da suke sayar da kayan da suka lalace ko marasa inganci ga al’ummar jihar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...