October 19, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Gwamnatin Kano ta Himmatu don Samun Nasarar Rigakafi a jihar – Dr. Tsanyawa

Gwamnatin Kano ta Himmatu don Samun Nasarar Rigakafi a jihar – Dr. Tsanyaw
 Gwamnatin jihar Kano ta sake jaddada kudirnta na tabbatar da samun nasarar rigakafin rigakafin yau da kullun .
 Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan yayin da taron yini 2 don tsara aikin rigakafi domin ci gaban Hukumar Kula da Lafiya matakin farko ta jihar Kano na Shekara ta 2021, Wanda ya gudana a otel din Asaa Pyramid da ke jihar Kaduna.
 Hon.  Kwamishinan ya jaddada cewa, gwamnatin jihar ta Kashe makudan kudade don inganta fannin kiwon lafiya, Inda ya kara da cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen yin duk Wani kokari na tabbatar da samar da tallafin da ya dace ga bangaren kiwon lafiya.
Cikin Wata sanarwa da Jami’in hulda da Jama’a na Hukumar kula da Lafiya a Matakin Farko ta jihar kano Maikudi Muhd Marafa ya aikowa Kadaura24 yace tsanyawa ya yabawa hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar bisa jajircewarta wajen daga darajar Hukumar zuwa matsayin da take a yanzu.
 A nasa jawabin tun da fari, Babban Sakataren zartarwa na hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Kano, Dakta Tijjani Hussain wanda Daraktan Gudanarwa da Kudi na Hukumar Alhaji Suleiman Tanimu ya wakilta, ya ce bunkasa tsarin aikin anyi shi ne da nufin samar da cikakken tsarin aiki don gudanar da ayyukan rigakafin yau da kullun.
 Daga nan Dr Hussain ya yabawa gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje saboda kulawa ta musamman da take baiwa Hukumar lafiya matakin farko.