October 19, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Ganduje ya baiwa Wata Yarinya rikon kwaryar Mulkin Kano

Wata yarinya Mai Suna Atika Aminu Yankaba Mai kimanin Shekaru 14 ta Zama Gwamnan jihar Kano na tsahon awa daya a Wani bangare na bikin ranar yara mata ta duniya wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 11 ga Watan octoba na kowacce shekara.
 Da take magana bayan karbe ragamar iko daga Gwamna Abdullahi Ganduje, Atika Yankaba ta kira taron Majalisar Zartarwa ta Jiha tare da sabbin mambobinta na majalisar kwamishinoni, tare da batutuwan ilimin yara mata da suka dauki mataki.
 Gwamna Atika Aminu Yankaba ta ce yayin da take jagorantar taron majalisar Zartarwar ta jihar ta buƙaci ƙarin kuɗi don gina ƙarin azuzuwan, ɗaukar ƙarin malamai da ba da fifiko ga ilimin na’ura Mai kwakwalwa.
 Hakanan, ta fada a cikin wani taron manema labarai cewa gwamnatin ta, wacce ta dauki tsawon awa daya kacal, za ta samar da dukkanin abubun da ‘ya’ya Mata suke bukata a jihar  domin Samar da ingantaccen ilimi ga mata.
 Tun da farko, Gwamna Ganduje ya ce yana mika mulki da son rainsa amma a takaice  “Ina zan dawo nan bada jimawa bada”.
 Lokacin da ya dawo Kan karagar Mulkin Kano, Gwamna Ganduje ya ce, “a lokacin da bana Kan kujerar nan, na shaida yadda kuka tafiyar da gwamnati kuma tsarin yayi kyau, an gudanar da taron majalisar zartarwa na ban mamaki, tare da dukkan kwamishinonin naga yadda Suka bayar da gudunmawa mai ban mamaki.”
Atika Aminu Yankaba ya rike Gwamnan Kano da misalin karfe 12:00 na Rana zuwa  kafin ya mayar wa Ganduje da karfe 01:00 na Rana.