Daga Safyan Dantala Jobawa
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ba da tabbacin ci gaba da aiki da Gidan Rediyon Tarayya Jewel FM Gombe da sauran ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da ke aiki a jihar domin cigaban jihar ta Gombe.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ba da tabbacin ne lokacin da ya karbi tawagar hukumar gudanarwa da ma’aikatan Gidan Rediyon Tarayya Jewel FM Gombe karkashin jagorancin Shugaban Gidan Radio kwamared Garba Ubale Danbatta .
Gwamnan ya yabawa gidan rediyon Jewel FM bisa irin gudunmawar da yake baiwa Jiha, inda ya baiyana shirye -shiryen tashar a matsayin masu fadakarwa, ilimantarwa danishadantarwaa .
Gwamna Inuwa ya ce duk da cewa Jewel FM mallakin Gwamnatin Tarayya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai tare da yin aiki tare da kafar domin ganin aiyukan da gidan yada labaran ke bayarwa suna da fa’ida ga Gwamnati da al’ummar jihar.
Gwamnan ya kara da cewa manufofi da shirye -shiryen gwamnatinsa da kuma na Jam’iyyar APC gaba daya za a iya yadasu ne ta hanyar kafafen yada labarai kawai.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta bayar da duk goyon bayan da ake bukata don maido da ofishin shiyyar gidan rediyon tarayya na FRCN zuwa jihar Gombe,inda nan ne asalin gurbin ofishin.
Gwamnan ya kuma umarci Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu Julius Ishaya Lapes da ya tsara hanyoyin yadda Gwamnatin Jiha za ta iya taimakawa gidan rediyon wajen biyan alawus -alawus ga ma’aikatan da ba na din din din ba.
Ya kuma umarci Kwamishinan ma’aikatar Gidaje da ya fara aikin kewaye harabar gidan rediyon na Jewel FM ba tare da bata Lokaci.
Tun da farko Shugaban Gidann Radiyon Tarayya Jewel FM Gombe, Kwamared Garba Ubale Danbatta ya sanar da Gwamnan cewa makasudin ziyarar da suka kai gidan gwamnati shine, godewa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya saboda goyon bayan da yake bawa tashar don ta tsaya da kafafunta.
Ya ce lokacin da ya shiga ofis a matsayin Babban Manaja na Jewel FM, tashar tana baya a bangaren kayan aiki na zamani wadanda zasu temaka wajen gudanar da aiki kamar yanda ya dace.
Babban manajan ya kuma baiyana cewa sanya hanun gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya cikin al’amuran gudan radiyon ya temaka wajen cigaban tashar musamman samun motar zirga zirga da sauran kayayyakin aiki.
Kwamared Danbatta ya tabbatarwa Gwamnan cewa tashar karkashin jagorancinsa tana gudanar da shirye -shirye da dama da nufin ilimantar da al’umma irin ayyukan da Gwamnati keyi a jihar.
A karshe Shugaban na Jewel FM, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta sake taimaka wa tashar ta hanyar yin shinge na kewaye tashar da kuma biyan alawu alawu ga ma’aikatan gidan radiyon da ba na din din din ba.
DIANABOL Inj. 100 mg buy online https://r1.community.samsung.com/t5/archive-forum/dianabol-inj-100-mg-buy-online/td-p/12826599
Where to buy steroids | Where to buy real steroids online forum? https://wheretobuysteroids2022.wordpress.com
Delta Airlines Phone Number | Delta airlines customer service phone number https://www.pinterest.com/pin/1071153092593253744/
Delta Airlines Phone Number | Delta airlines customer service phone number https://sites.google.com/view/delta-airlines-phone/
Delta Airlines Phone Number | Delta airlines customer service phone number https://delta-airlines-phone-number.business.site
Delta Airlines Phone Number | Delta airlines customer service phone number https://sakarea2.go.th/community/profile/delta-airlines-phone-number/