Daga Sani Danbala Gwarzo
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya Sauke ministocin wutar lantarki da aikin gona.
Shugaban ya sauke Saleh Mamman da Sabo Nanono daga mukamansu na majalisar ministoci a ranar Laraba.
An bayyana ministan muhalli a matsayin ministan gona, yayin da aka nemi karamin ministan ayyuka da gidaje ya yi aiki a matsayin karamin ministan wutar lantarki.
Shugaba Buhari ya kuma sauya ministan muhalli, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar zuwa ma’aikatar noma da raya karkara, da karamin ministan ayyuka da gidaje, Engr. Abubakar D. Aliyu, zuwa Ma’aikatar Wutar Lantarki.
Allah yasa albarka mai yawa cikin wannan mulkin