Zargin Rashawa: IG ya bada Umarnin binciko Gaskiyar zargin da akewa Abba kyari

Date:

Babban Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan tuhumar da hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a Amurka take yi wa fitaccen dan sanda DCP Abba Kyari.

Hukumar ta FBI tana tuhumar Kyari da laifin hannu a ayyukan damfara da take binciken Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi, matashin nan mai arziki dan Najeriya da hukumomin Amurkan suka kama suke kuma tuhumar yanzu haka a Amurka, bisa aikata laifukan da suka shafi zamba da damfara ta yanar gizo.

“Bayan da muka samu bayanai kan zargin tuhumar da hukumar hukunta manyan laifuka ta FBI take yi wa daya daga cikin jami’anmu, Sufeto Janar na ‘yan sanda IGP Usman Alkali Baba, ya ba da umarnin a gudanar da binciken cikin gida kan lamarin.” Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Najeriyar ta fitar dauke da sa hannun kakakinta CP Frank Mba ta ce.

“’Rundunar ‘yan sandan Najeriya na kara jaddada cewa ta himmatu wajen tabbatar da adalci da karfafa dangantakar da ke tsakaninta da FBI da sauran abokanan hulda na kasa da kasa.” Mba ya ce.

Sashin Hausa na Murnar Amuruka ya rawaito cewa Rundunar ‘yan sanda Najeriyar ta ce, za ta bayyanawa jama’a duk abin da ya taso dangane da wannan lamari idan ta kammala gudanar da bincikenta.

Hushpuppi ya shiga hannun Amurka ne a watan Yunin shekarar 2020 bayan da ‘yan sandan Hadaddiyar Daular Laraba suka kama shi a Dubai.

A wani zaman kotu da aka yi a ranar Laraba 28 ga watan Yul

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...