Tsokaci kan talla ga yara ƙanana Nasara ko Asara ?

Date:


Daga Zaiyad Ismail Yola:

Talla wata a’lada ce da ake dora wa kananan yara abubuwan sayarwa domin su rika yawo kwararo-kwararo suna sayarwa da zimmar samun abin sanya wa a bakin salatin ga iyayensu.

Kananan yaran da shekarunsu suka kama daga biyar sukan dauki tallan abinci da abin sha
inda suke tafiya kasuwa da wuraren tarukan jama’a domin sayarwa.

Hakan yakan karfafa gwiwar iyayensu su ci gaba da dora musu talla da zimmar samun kudin yin kayan daki idan lokacin auren yarinyar ya zo.

Iyayen sun yi amannar cewa tara irin wadannan kudade da aka samu daga talla na taimaka musu wajen fita kunya loakcin auren yaran.

Shi hakan gaskiya ne?
Ko dai wata dabara ce da iyayen ke amfani da ita wurin ajiye nauyin da ya rataya a wuyansu na ciyar da kuma tufatar da ‘ya’yansu musamman mata?

Ko da a cikin dabbobi, babban nauyin da ya rataya a wuyan iyaye shi ne kula da ‘ya’yansu.
Don haka nauyin da ke wuyan iyaye shi ne kula da ‘ya’yansu. Amma me ya sa iyayen wadannan ‘yan mata da ke tallace-tallace suke yin watsi da wannan nauyi?

Wasu na da ra’ayin cewa hakan na faruwa ne saboda talauci. Sai dai wasu na sukar iyayen da cewa sakaci da rashin son daukar nauyin da Allah yarata akansu ne ke haddasa tallace-tallace

Hakazalika wasu na ganin laifin al’umma da gwamnati ne, wacce alhakin kula da jama’a ya rataya a wuyanta.

Koma dai mene ne dai, abin da ya fito fili shi ne yawon tallace-tallace a wurin ‘ya’ya mata, har ma da mazan, yana jefa su cikin hadarin fuskantar fyade da musgunawa da ma sace su.
Don haka mecece makomar wadannan yara da ke gararamba a titi maimakon zuwa makaranta?

145 COMMENTS

  1. Ковалев Про Бой Усик – Джошуа, «Удачи, Саня» – Бокс/Mma Александр Усик Энтони Джошуа DAZN Обязательный претендент на титул wbo в супертяжелом весе Александр Усик уверен, что они с чемпионом мира по версиям wba, wbo, ibo и ibf Энтони Джошуа устроят поединок, который навсегда останется в истории.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...